Tun Adamau da Hawwa'u zuwa ga Manzo Yohanna, ana samun addu'a duk cikin Maganan Allah. Yawancin mu mun san addu'a na da muhimmanci, amma sai mu samu kanmu muna gwagwarmaya da sa shi na farko a cikin rayuwan mu na kullum Saboda haka, sai mu kusaci kursiyin Allah na alheri da amincewa, domin a yi mana jinƙai, a kuma yi mana alherin da zai taimake mu a kan kari. Ibraniyawa 4:16 Cikin addu'a, akan gayyace mu mu samu zumunci da Allah yayinda mu ke kusance Shi, muna amincewa da sanin mu na bukatan kasancewan Shi a cikin rayuwan mu Amma duk da wannan sani, dayawa daga cikin mu na gwagwarmaya da yin amfani da wannan zarafi. Cikin rashin sanin mu, sai mu na yi kamar mu na da karfin kawas da jaraba, ko mu na da karfin yaki da harin shaiɗan, ko mu na da wayo sosai da za mu iya samun hanyan mu da kan mu cikin wannan duniya, ku mu na da ilimi sosai da za mu iya gane ma'anar Maganar Allah da kan mu. Allah bai so mu yi rayuwa haka ba. Idan ki na bukatan ki kusanci Mai Ceton ki ta wurin sa addu'a ya zama babban muhimmanci a rayuwan ki, to Muhimmancin Addu'a an yi ne domin ki. A cikin wannan binciken Littafi mai Tsarki na tsawon mako shida daga Love God Greatly, za mu ɗauki lokaci cikin Maganan Allah, za mu nemi amsoshi ga tambayoyi game da yadda yakamata mu yi addu'a, da yadda zamu sa addu'a ya zama da muhimmanci, da kuma ko Allah Ya na ji ko ba Ya jin addu'o'in mu. Mu yi bincike tare yayinda mu ke shiga cikin Maganan Allah, cikin karatu da rubuta abin da Allah ke faɗa wa zuciyar mu. Mu na begen za ki haɗa kai da mu a yanan gizo domin wannan binciken Littafi mai Tsarki na tsawon mako shida ko kan app namu na Love God Greatly. Za ki samu abubuwan da ya shafi Muhimmancin Addu'a a duka wurare biyu tare da rubuce rubucen mu na Litinin, Laraba da Jumma'a, kari bayani ta wurin karatu na kullum da kuma jama'a masu kauna domin su yi tafiya da ke yayinda ki ke binciken muhimmancin addu'a!
All of the products displayed on this website are supposed to be Christian.
However, occasionaly some products get added and slip through our automated content filters unnoticed by our Admins.
If you notice anything that shouldn't be here, please help us out and let us know by clicking the following button:
Flag this Product